A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, wannan kwas din wanda aka fara kusan wata daya da ya gabata, Cibiyar Musulunci ta Kasa da Kasa ce take gudanar da shi. Manufar taron ita ce yada ruhin zaman lafiya a kasar Brazil da kuma yankin Amurka ta Kudu, kuma abin farin ciki ne yadda iyalan musulmi suka karbi wannan shiri hannu bibbiyu. Ana gudanar da wadannan azuzuwan sau da dama a mako kamar yadda aka tsara, inda ake samar wa yara da matasa yanayi mai kyau na ilimi da zumunci.
Tsarin karatun ya kunshi:
Haddar Al-Kur'ani da dokokin Tajwidi.
Bayani kan Hadisai guda arba'in (40) da aka zaba daga Manzon Allah (S.A.W).
Darussan Ilimin Kalam (Tauhid), Fikihu, Akhlak (Dabi'u), da kuma sanin addini na bai daya.
An tsara wadannan ayyukan ilimi ne ga rukunin shekaru daban-daban domin karfafa musu gwiwar shiga cikin harkokin addini.
Wasu daga cikin manyan malamai da masu wa'azi a Brazil sun gabatar da jawabi a wurin taron kaddamar da shirin, a karkashin jagorancin Abdulhamid Mutawalli, shugaban cibiyar. An tsara cewa wannan shirin zai ci gaba har zuwa karshen watan Janairu, inda za a kammala shi da taron karrama daliban da suka nuna kwazo.
Your Comment